1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Jamus da Iraq za su yi aikin hadin gwuiwa

Zulaiha Abubakar
April 22, 2018

Kasahen biyu sun amince da suyi aiki tare don mayar da 'yan gudun hijira da kuma sake ginin kasar ta Iraqi wace tayi fama da yaki.

https://p.dw.com/p/2wTet
Gerd Müller ministan raya kasa na Jamus
Gerd Müller ministan raya kasa na JamusHoto: picture-alliance/dpa/R. Jensen

Wannan sanarwa na zuwa ne yayin da ministan raya kasa na Jamus Gerd Mueller ya gana da firaministan Iraqi Haider al-Abadi yau lahadi a birnin Baghdad dake kasa ta Iraqi. Tun da fari kafin ziyarar ta sa ministan raya kasar na Jamus ya shaida wa manema labarai a jiya Asabar cewar abu ne mai muhimmancin gaske yadda al'umma ke iya komawa garuruwan su don ba 'ta'addanci kunya,daga nan sai ya kara jaddada aniyar kasashen na ba ilimi fifiko,a wani ci gaban kuma sama da mutane dubu goma 'yan kasar Iraqi mazauna Jamus za su amfana da taimako daga Jamus don su koma gida.