Kasashen Larabawa da batun yakin Siriya
March 27, 2017Ahmed Abul Gheit wanda kuma shi ne ministan harkokin kasashen ketare na kasar Masar, ya yi wannan kiran ne a wajen taron share fage da ministocin kasashen ketare na kasashen Larabawan ke yi. Da yake tsokaci kan rikicin na Siriya da Yemen da kuma Libiya mai masaukin baki, ministan harkokin kasashen ketare na Jodan din Ayman Al-Safadi cewa ya yi:
"Duk mun amince cewa tilas a kawo karshen zubar da jini a Siriya a siyasance kamar yadda aka amince a taron Geneva karo na farko da kuma kudirin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na resolution 2254, domin tabbatar da hadin kai a Siriya da kuma samun 'yancin kai. Haka kuma muna bukatar samun mafita karkashin dokokin kasa da kasa a Yemen da tabbatar da ganin an cimma yarjejeniyar sulhu, haka ma abin yake kan batun rikicin Libiya."
Kasar Siriya dai ba ta samu gayyata a wannan taron ba, kasancewar kungiyar kasashen Larabawan ta dakatar da ita tun a karshen shekara ta 2011 bayan barkewar juyin-juya hali a kasar.