Kasashen Larabawa za su yi zama kan Iran
November 12, 2017Talla
Kungiyar kasashen Larabawa ta bayyana cewa za ta yi wani zaman gaggawa a ranar Lahadi ta mako mai zuwa bayan da kasar Saudiyya ta bayyana bukatar hakan. Wannan zama dai a lokacinsa za a tattauna kan abin da suka kira wuce makadi da rawa da kasar Iran ke yi musu a yankin kamar yadda ajandar taron da wani jami'in diplomasiya ya nunawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ta nunar. Kasar Bahrain da Daular Larabawa ta UAE sun nuna goyon bayansu ga bukatar ta Saudiyya kamar yadda ita ma Djibouti da ke jan ragamar kungiyar a yanzu ta nuna goyon baya. Takaddamar baya-bayan nan dai ta taso ne bayan da shugaban kasar Lebanon ya zargi Saudiyya da yin garkuwa da firaministan kasar da ya yi murabus yayin da yake wata ziyara a Saudiyyan.