Kasashen musulmi sun yi kira da a warware rikicin nukiliyar Iran cikin lumana
February 25, 2007Wasu manyan kasashen musulmi guda 7 sun yi kashedi game da tabarbarewar takaddamar da ake yi akan shirin nukiliyar Iran. Wata sanarwar bayan taron ministocin harkokin ketare na kasashen musulmin da aka gudanar a Islamabad babban birnin kasar Pakistan, ta yi kira da a yi amfani dukkan hanyoyin diplomasiya don warware wannan takaddama. Ministocin suka ce ko kadan bai kamata a yi amfani da karfi ba. Ministocin na kasashen Saudiya, Turkiya, Indonesia, Malyasia, Jordan da kuma Masar sun je Islamabad ne don shawartawa da takwaransu na Pakistan akan daukar dubaru na bai daya game da yankin GTT. A wani labarin kuma sakatariyar harkokin wajen Amirka C-Rice ta gargadi hukumomin Teheran da ka da su mayar da kasar su saniyar ware a dangane da manufofinsu na nukiliya.