Kasashen Nahiyar Afrika sun koka kan Asusun IMF da Bankin Duniya.
March 30, 2004Sakamakon ci da gumi da kasashe maso tasowa na nahiyar Africa ke ganin kasashe masu arzikin masana,antu na duniya nayi musu dangane da mamaye madafun ikon tafiyar da harkokin Bankin duniya da kuma bankin bada lamuni na duniya,a yanzu haka kasashen sun fara daukaka kira na shigo dasu dairar yadda ake gudanar da harkokin don a dama dasu.
Rahotanni dai sun nunar da cewa da dama daga cikin kasashen na Nahiyar ta Africa sun nuna bacin ransu dangane da yadda ake zabar shugabannin hukumomin guda biyu,da cewa akwai son kai da kuma zalumci a cikin sa.
Hakan a cewar rahoton baya bawa ire iren kasashen na nahiyar ta Africa wakilcin daya dace a cikin hukumomin biyu,wanda hakan a ganin su shi yake kara jefa su a cikin duhu na rashin sanin irin wainar da ake toyawa dangane da tattalin arzikin duniya baki daya.
A cewar ta bakin mai magana da yawun ire iren wadan nan kasashe na kudancin nahiyar ta Africa,Ariel Buira,cewa yayi kamata yayi ace ana gudanar da zaben shugabannin wadan nan hukumomi ne ta hanyar gaskiya da kuma adalci,ta yadda kowane bangare na duniya ba zaice anyi masa saniyar ware ba.
Kakakin kasashen masu tasowa na Africa ya kara da cewa kashi 80 zuwa 85 na mutanen dake rike da mukamai iri daban daban a wadan nan hukumomi biyu sun fito ne daga kasashe masu arzikin masana,antu na duniya.
Mr Ariel yaci gaba da cewa a yanzu haka kasashen maso tasowa sun dauki aniyar ganin cewa a zaben shugaba na bankin bada lamuni na nan gaba da zaayi,dan nahiyar ta Africa ne zai samu nasarar darewa kujerar ba wani daga wata kasa a kasashen yamma ba.
Shi kuwa Datlef Kotte jamii dake aiki a kwamitin dake kula da saye da sayarwa na mdd,cewa a tun bayan da aka kafa wadan nan hukumomi biyu kasashen nahiyar Africa sun kasance kasashe da sukafi ko wadanne kasashe na duniya Amfanar hukumomin.
A misali a cewar Mr Kotte a yau an wayi gari da cewa kusan shekaru 25 da suka wuce babu wata kasa daga cikin kasashe masu tasowa data karbi bashi daga daya daga cikin wadan nan hukumomi.
A don haka a ganin sa kasashen na Nahiyar ta Africa zasu fi son ko wace kasa ta duniya ganin wadan nan hukumomi sun samu inganci daci gaba,ta hanyar samar da shugabanci na gari.
Jamiin yaci gaba da cewa a lokacin da aka kirkiro wadan nan hukumomi kasar Amurka ta kasance kasa dake da yawan jari a cikin sa,amma a yau an wayi gari da cewa tafi ko wace kasa ta duniya cin bashi,to amma fa ba daga wadan nan hukumomi ba.
A dai wan nan shekarar ne nan gaba ba da dadewa ba ake sa ran daya daga cikin shugabannin hukumomin wato Horst Koehler zaiyi murabus daga mukamin sa don tsayawa takarar neman shugaban cin kasar Jamus karkashin hadin gwiwar jamiyyun adawar kasar.
Dalilin hakan ne da kuma wasu dalilai na sama da muka zayyana masu nazarin abin da kaje yazon ke ganin ya kamata ace a wan nan lokaci an shigo da kasashen na nahiyar Africa cikin shugabanci don a dama dasu,musanmamma don sanin inda tattalin arzikin duniya yasa a gaba.