Bukatar hana kyamar addini a duniya
July 12, 2023Talla
Wannan matakin da kwamitin Kare Hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniyar ya dauka yayin taronsa dai na zuwa ne, daidai lokacin da ake fuskantar kona al-Qur'ani a kasashen Turai. Kasashen Yamma dai sun nuna adawarsu da matakin, inda suka ce daukar tsauraran matakai a bangaren gwamnati ka iya yin illa ga 'yancin fadar albarkacin baki. An dai kaure da tafi a yayin taron, bayan da kasashe 28 mabobin kwamitin suka amince da matakin yayin da 12 suka kada kuri'ar kin amincewa bakwai kuma suka yi rowar kuri'unsu. Falasdinu da Pakistan ne dai suka kawo kudirin gaban kwamitin, yayin da suka samu goyon baya daga kasashe masu tasowa na Afirka da Chaina da Indiya da kuma kasashen yankin Gabas ta Tsakiya.