Kasuwancin makamai tsakanin China da Rasha
May 15, 2024Wannan ziyara ta Vladmir Putin na zuwa ne bayan ya nada wani na hannun damansa kana masanin tattalin arziki Andrei Beloussov a matsayin sabon ministan tsaron kasa.
Wani sabon bincike da aka gudanar a Amurka ya nuna cewa, kasar China ta kasance kasa mafi muhimmanci wajen samar da na'urorin lantarki da kuma na'urorin da ake kera makamai tun daga shekarar ta 2023 ga kasar Rasha.
A ƙarshen shekara ta 2023, wata cibiyar bincike da kula da harkokin ketare ta Jamus (DGAP) ta gudanar da wani bincike wanda a cikinsa ta ce nan gaba Rasha tana iya kai wa daya daga cikin kasashe manbobin NATO hari. Christian Mölling shi ne shugaban cibiyar
A karshe dai abin da za a iya cewa shi ne Putin da yakin yake rayuwa. Yana bukatar yakin domin cimma manufofinsa wanda kuma babu wani fata na samun zaman lafiya a gareshi
A yanzu haka dai NATO na Shirin kaddamar da wani shiri na samar da makamai ga kasashe 50 masu goyon bayan Ukraine karkashin jagorancin Amirka don kare kai.
Tun bayan da Rasha ta fara mamaye kasar Ukraine a cikin watan Fabrairun shekara ta 2022. Rasha ke shigar da kayan lantarki daga China, domin kauce wa takunkumin kasashen yamma. Masu bincike na wata hukumar Amirka CSIS sun ce Rasha na sayen rokoki da bama-bamai da injinan sarrafa na'ura mai kwakwalwa da sauraran abubuwa da ake kera makamai da su daga China.
Saboda haka, kasar China na da muhimmanci ga Rasha domin kusan dukkanin manyan masu fitar da na'urorin lantarki na micro-electronics suna zaune ne a China da Hong Kong, kuma kamfani guda yana da tushe a Turkiyya.
Vladislav Vlasiuk, masanin takunkumin karaya tattalin ariki a Ukraine ya yi tsokaci da cewar
"Yawancin babu wani abu da Rasha da kanta take kerawa, kusan ba komai. Idan gobe duk kayayyakin da ake shigowa da su Rasha aka tsaida ba za su iya kera makaman ba."
Tun daga farkon shekarar 2024, sojojin saman kasar Rasha ke kara samun nasara wajen yin galaba a kan tsaron sararin samaniyar kasar Ukraine, sakamakon yadda Rashar ke samu makamai masu linzami daga China don haka za a iya cewar ziyarar ta Putine a China na muhimmanci sosai