Kawancen Britaniya da Pakistan wajen yaki da taáddanci
November 19, 2006Talla
Kasashen Britaniya da Pakistan sun ci alwashin yin aiki tare ya zuwa shekaru masu zuwa domin yaki da taáddanci da kuma tsatsauran raáyin addini. P/M Britaniya Tony Blair tare da shugaban kasar Pakistan Pervez Musharraf sun sanya hannu a kan wata sanarwar hadin gwiwa bayan da suka kammala ganawa a birnin Lahore. Ganawar ta maida hankali ne a kan hada karfi wuri guda da musayar bayanan sirri domin shawo kan tawayen yan Taliban a Afghanistan da kuma sake fasalin manhajan ilimin Pakistan masu sassaucin raáyi.