Kawancen NATO na bukatar a karbi Ukraine
April 21, 2023Sakataren kungiyar kawancen tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya ce kasashe mambobin kungiyar sun amince Ukraine ta shiga cikin kawancen kungiyar sai dai babban abin da kungiyar ta mayar da hankalinta a kai a yanzu shi ne rikicin da ke tsakaninta da Rasha.
Ya yi wannan kalamin ne ga 'yan jarida a Ramstein gabanin taron da kungiyar za ta gudanar a wannan juma'ar a Jamus.
Stoltenberg din dai bai jima da dawowa daga Kiev ba inda shugaban Ukraine ya yi kiran gaggauta shigar da kasarsa cikin kawancen kungiyar tsaron.
Daya daga cikin sharuddan shiga kungiyar tsaron ta NATO shi ne kasa ta kasance bata cikin yaki.
Tuni dai ministan tsaron Jamus Boris Pistorius ya ce babu tabbas game da shigar Ukraine cikin kungiyar a halin yaki da Rasha.
Pistorius ya ce ba ma za a kawo batun a Jadawalin batutuwan da taron zai tattauna ba.