Kawancen yaki da ta'addanci tsakanin Nijar da Mali
March 27, 2023Nasarar da sojojin Nijar na rundunar operation Guguwa ko Almahaou suka samu ta halaka 'yan ta'adda 71 da lalata babura kimanin 200 a harin da suka kai har maboyar ‘yan ta'addan a garin Hamakat na kasar Mali ya faranta ran ‘yan Nijar da dama musamman dangane da yadda kasar Malin ta bai wa sojojin Nijar izinin shiga har cikin kasarta domin farautar ‘yan ta'adda wadanda suka halaka sojojin Nijar 17 a wani harin kwantan baunar da suka kai masu a ranar 23 ga watan Fabrairun 2023 a kauyen Intagamey na jihar Tillabery.
Malam Massaoudou wani mai sharhi kan harkokin yau da kulluma Nijar ya ce dama irin wannan tunani ya kamata shugabannin kasashen biyu su yi domin tunkarar matsalar tsaro.
‘Yan Nijar da dama dai na zargin kasashen Faransa da Rasha da kasancewa ummulhaba'isin zaman ‘yan marina tsakanin Nijar da Mali wanda ya bai wa 'yan ta'addar da ke zaune a arewacin Mali damar ketarowa zuwa cikin Nijar inda suka kashe sojoji da fararan hula da kuma kore dabbobi zuwa cikin Mali ba tare da Nijar din ta iya daukar mataki ba.
Alhaji Idi Abdou wani dan fafutuka a Nijar ya ce lokaci ya yi da kasashen biyu za su tilasta wa abokan huldar su Rasha da Turai kiyaye huldar gado da ke tsakanin kasashen biyu.
Da yake tsokaci kan wannan batu, Kalla Moutari dan majalisar dokoki kuma tsohon Ministan tsaro a Nijar, cewa ya yi dama akwai yarjejeniyar farautar ‘yan ta'adda cikin kasashen juna tsakanin Nijar da Mali, amma Nijar ta daga kafa ne a bisa rashin sanin matsayar sabbin hukumomin Mali kan wannan yarjejeniya.
Yanzu dai fatan jama'a shi ne su ga ranar da sojojin kasashen biyu da na makobciya kasar Burkina Faso za su fara aiki tare wajen soma kwato arewacin kasar Mali daga ‘yan ta'adda da ke zama sharadi na samun sa'ida a kasashen uku masu tarayya a hukumar Liptako Gourma.