Matakan yaki da kyamar masu HIV/AIDs
July 23, 2018Wata kafar fidda bayanai kan bazuwar cutar a duniya ta "Global Information and Education", ta nunar cewa Najeriya har yanzu da sauranta kan kokarin da take domin fuskantar matsalar yaduwar cutar ta HIV/AIDs ko SIDA cikin kasa, musammanma yadda mutane da daman ke ta nuna halin ko in kula ga irin wayar da kan da ake ta faman yi, lamarin da ke kara haifar da fargaba na kara yada cutar a tsakanin al'umma. Uwar gida Fortune Kallio, wata ce da ta sadaukar da kanta wajen hada hannu da hukumar hana bazuwar cutar ta HIV/AIDs ko SIDA ta SACA a jihar Rivers, inda kuma kungiyarta ta "Save my Soul" ke kokarin bada gudunmawa a tsakankanin matasa kan cutar inda take cewa: "Muna kokarin gano wadanda suke dauke da cutar tare da ba su karfin gwiwar cewa za su iya rayuwa mai kyau, tare da tabbatar da cewa suna samun magunguna kuma suna shan magungunan kamar yadda ya kamata, gami da ba su shawarwari da samar musu da kungiya da za ta rinka tallafa musu a tsawon rayuwarsu cikin wannan cuta."
Gwamnatin Amirka dai ta bayar da gudummawar Dala miliyan 90, kwatankwacin Naira miliyan dubu 32 ga Najeriya domin aikin gano masu dauke da cutar ta HIV/AIDs ko SIDA a fadin kasar tare da tantance su.