Kawo karshen ayyukan rundunar MONISCO a Kwango
August 12, 2023Talla
A wani rahoto da ya gabatarwa kwamitin sulhu na MDD, Guterres ya bayyana shirin da ma tsare-tsaren janye rundunar MONUSCO bayan kwashe kusan shekaru 25 tana aiki a kasar.
Rahoton mai shafuka 15 ya nuna yadda cin zarafin mata da kananan yara ya rubanya daga shekarar 2021 zuwa 2022.
Kazalika ya yi gargadin lamuran tsaro a kasar da ta jima tana fama da rikici na ci gaba da tabarbarewa.
Yankin kudancin Kivu da Ituri na daga cikin yankunan da lamarin ya fi kamari, inda sama da kaso 28 zuwa 39 na al'ummar yankin rikici ya raba su da matsugunnansu.