1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a dage wa Iran takunkumin makamai

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 15, 2020

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya sanya kafa ya yi fatali da bukatar Amirka na tsawaita wa'adin takunkumin makamai da aka sanyawa kasar Iran.

https://p.dw.com/p/3h0cj
USA Übersicht UN-Sicherheitsrat | "Maintenance of International Peace and Security"
Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya juyawa Amirka bayaHoto: AFP/S. Platt

Rahotanni sun nunar da cewa yayin kada kuri'a kan batun, kasar Jamhuriyar Dominika ce kadai ta marawa Amirka baya. A nasu bangaren, kasashen Chaina da Rasha sun kada kuri'ar kin amincewa yayin da kasashe 11 da suka hadar da Jamus da Faransa da Birtaniya suka yi rowar kuri'unsu. Tuni dai Amirkan ta mayar da martani kan matakin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniyar, ta bakin sakataren harkokin kasashen ketarenta Mike Pompeo wanda ya bayyana matakin da wata gazawa maras dalili.

A nata bangaren Iran ta yaba da matakin kwamitin sulhun, tana mai cewa Amirka ba ta taba ganin an juya mata baya kan bukatunta kamar a wannan karon ba. Kakakin ma'aikatar harkokin kasashen waje na Iran din Abbas Mousavi ya wallafa a shafinsa na Tweitter cewa, a karon farko cikin tarihin Majalisar Dinkin Duniya tun bayan kafata shekaru 75 da suka gabata, an nunawa Amirka wariya ta ban mamaki. A shekara ta 2015 ne dai aka amince da cewa wa'adin takunkumin sayar da makaman kan Iran zai kare a watan Oktobar wannan shekarar ta 2020, bayan cimma yarjejeniyar nukiliyar Iran din da Amirka ta yi watsi da ita daga baya, wa'adin kuma da Amirkan ta bukaci a tsawaita shi.