1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin kawo karshen rikicin Siriya da ke lakume rayuka

Lateefa Mustapha Ja'afarMay 11, 2015

Bangaren da ke wakiltar 'yan tawayen Siriya ya ce ba zai halarci taron share fage na sake tattauna batun rikicin kasar ba.

https://p.dw.com/p/1FOD4
Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Siriya Staffan de Mistura
Hoto: Fabrice Coffrini/AFP/Getty Images

Majalisar Dinkin Duniya ce dai ta kaddamar da wannan tattaunawa a birnin Geneva a makon da ya gabata. Wani mamba a kungiyar hadaka ta Syrian National Coalition Samir al-Nashar ya sanar da cewa bangaren nasu da ke da goyon bayan kasashen yamma da kuma kasashen Larabawa bai ji dadin yadda aka gayyaci Iran da ke goyon bayan gwamnatin Shugaban Bashar al-Assad na Siriyan don ta halarci taron ba. Al-Nashar ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na nan Jamus DPA cewa kungiyarsu na fargabar ba za a yi mata adalci ba duba da yadda aka gayyaci bangarori da dama wajen wannan tattaunawar da bata kai tsaye ba, wadda ake fatan ita ce za ta share fagen shiga ka'in da na'in cikin tattaunawar sulhu da ka iya kawo karshen zubar da jinin da aka kwashe tsahon shekaru hudu ana yi a Siriyan.