Kenya: Zanga zangar tsadar rayuwa da haraji
July 20, 2023Tun a watan Maris din ya gabata ne dai jagoran 'yan adawar Kenya Raila Odinga ya jagoranci jerin zanga-zanga a kasar. Dama dai jam'iyyar Odinga ta bukaci mutane su fito kwansu da kwarkwata. Sai dai duk da wannan kiraye-kiraye,gwamnatin kasar ta bukaci sake bude makarantu da kuma shaguna a biranen Nairbi, Kisumu da kuma Mombasa. Ma'aikatar cikin gida ta tabbatar da kare lafiya da dukiyoyin jama'a da kuma daukar dukkanin matakan da suka dace.
'Yan sanda sun tarwatsa masu boren inda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye da ma yunkurin amfani da karfi wajen dakile zanga zangar. Masu boren sun yi kira ga shugaban kasar William Ruto da ya sake fasalin dokar sanya kudaden haraji. Rahotannin sun yi nuni da cewa kimanin mutum biyu sun rasa rayukansu yayin da wasu biyar suka jikkata a arangamar a birnin Nairobi.
A makon da ya gabata ma an gudanar da makamanciyar wannan boren da ta yi sanadiyyar rayukan mutane shida yayin da wasu kananan yara 56 da suka shiga mawuyacin hali bayan shakar barkonon tsohuwa.
Jama'a da dama na baiyana bukatar bangarorin biyu su nuna halin dattako
Wycliffe Onyango, mazaunin Nairobi ke cewa "Dukkanin abun da muka samu muna kashewa ne wajen sayen abinci, a yanzu haka ba a samun aikin yi. Ina rokon gwamnati ta kawo karshen tsadar rayuwa da ake fuskanta. Shugaba Willam Ruto da kuma madugun adawa Raila Odinga su zauna kan teburin sulhu. Gwamnati da daina dukar mutane ta na hanasu kuka"
Kimanin mutane 300 ne aka kama a zanga-zanga bisa zargin laifi kwasar ganima da fashi da kuma kai hare-hare. Shugaba Ruto ya bukaci jami'an tsaro su dauki mataki kan 'yan daba da kuma mutanen da suke tada zaune tsaye. Dama dai gwamnatin ta zargi 'yan adawa da kokarin kawo cikas ga inganta tattalin arzikin kasar. Tuni dai kasashen duniya suka fara yin kira ga bangarorin kasar kan su dinke barakar da ke tsakaninsu. Sheikh Amza na daga cikin 'yan kasar da ke ganin hakan ne mafita.
" Ba na goyon bayan zanga-zanga kuma bana goyon bayan wannan tsadar rayuwar da ake fuskanta. Yana da kyau a samu masalaha ta hanyar zama kan teburun tattaunawa domin samun mafita. Rasa rayuka da kuma lalata dukiyoyi ba zai taba taimakawa ba. Mun ga yadda mutane ke mutuwa wanda hakan abin tashin hankali ne."
Shugaba William Ruto dai ya yi alkawarin rage radadin talauci a kasar, sai dai al'umma na cewa kullum farashin kayayyakin na kara tashi a kasuwanni karkashin gwamnatinsa.