Kenya: Mutum 18 sun mutu a rikicin kabilanci
October 12, 2024Ministan harkokin cikin gida na Kenya, Kithure Kindiki ya ayyana yankuna 12 da ke kusa da kogin Tana a matsayin wurare mafi hadari a kasar sakamakon rikice-rikicen da ya addabi makiyaya a yankin. Tuni shugaban Rundunar 'yan sandan kasar, Douglas Kanja ya bukaci dukannin mazauna yankunan su mika makamansu domin dakile kara rincabewar rikici.
Karin bayani: Rigingimun siyasa na ci gaba da janyo mutuwar jama'a a Kenya
Rikicin da ya fi kamari a yankin Bura, ya samo asali ne bayan da gwamnatin kasar ta bayar da fili domin sake matsagunni ga al'umomin da iftila'in ambaliyar ruwa ya raba su da matsugunnansu a gabar kogin Tana da ke kasancewa ruwa mafi tsawo a kasar Kenya. Sai dai makiyaya a yankin na cewa mutanen da aka sauya wa matsagunnai za su mamaye wuraren kiwon su ne.
Kawo yanzu dai, daractar sashin binciken miyagun laifuka na kasar, Mohamed Amin ya bayar da umurnin kama shugabannin yankunan biyu da ke gabar kogin, sakamakon rashin amsa gayyatar da rundunar 'yan sanda ta musu kan rikicin yankin.