Kenya ta harba tauraron dan Adam na farko
April 15, 2023Talla
Kasar Kenya ta kaddamar da taurarun dan Adam na farko wanda kwararrun masana kimiyya 'yan asalin kasar suka kirkiro.
Tauraron na dan Adam wanda kamfanin Space X ya harba daga birnin California na kasar Amurka, an kera shi ne da nufin samun bayanan kimiyya da za su inganta harkokin noma da ma sa ido kan al'amuran da suka shafi muhalli.
Sau da dama ne aka yi ta dage aikin harba tauraron zuwa sararin samaniya cikin wannan makon, saboda rashin kyawun yanayi.
Kasar ta Kenya dai na daga cikin kasashen yankin gabashin Afirka da ke fama da matsaloli na yanayi, musamman na bala'in fari da ke haddasa tsananin karancin abinci da ma ke kare dabbobi.