1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya ta kafa dokar takaita fita a Mandera

October 27, 2016

Gwamnatin Kenya ta kakaba dokar takaita zirga-zirga har na tsawon kwanaki 60 a garin Mandera da ke arewa maso gabshin kasar, sakamakon matsin lamba na 'yan ta'adda.

https://p.dw.com/p/2RmwO
Kenia Angriff auf Busse in Mandera
Hoto: picture-alliance/dpa

Wannan mataki dai na zuwa ne bayan da yankin na Mandera da ke kan iyaka da Somaliya ya fuskanci munanan hare-haren kunar bakin wake har guda biyu cikin makoni uku, musamman harin da Kungiyar al-Shabab ta kai a baya-baya nnan da ya hallaka mutane 12.

Da ya ke karin haske kan dokar, ministan cikin gida Joseph Nkaissery, ya ce daga yau Alhamis dokar za ta fara aiki daga karfe 6.30 na yamma zuwa 6:30 na safe har sai 27 ga watan Disamba da ke tafe. Ana dai alakanta kungiyar 'yan ta'adda na Al-Qaeeda da dasawa da  al-Shabab wacce ta sha alwashin ganin bayan gwamnatin Somaliya.