Kenya ta rufe iya da makobtanta sabilin Corona
May 16, 2020Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya dauki matakin rufe iyakokin kasa na tsakanin kasarsa da makobtanta na Tanzaniya da Somaliya tare da tsawaita har zuwa shida ga watan Yuni wa'adin dokar kulle da takaita zirga-zirga a wani yinkuri na neman dakile annobar cutar ta Covid 19 wacce kawo yanzu ta harbi mutane 830 ta kuma halaka 50 a kasar.
A wani jawabi da ya gabatar a tashar talabijin ta kasa, Shugaba Kenyatta ya ce matakin ya tanadi dakatar da duk wani kai kawon jama'a da zirga-zirgar motoci ban da masu jigilar kayan masarufi a tsakanin kasar da makobtanta na Somaliya da Tanzaniya.
Shugaba Kenyatta ya ce dauki wannan mataki ne bayan da bincike ya nunar da cewa daga cikin mutanen 166 da suka harbu da cutar a wannan mako a kasar, 43 sun shigo ne daga kasashen na Somaliya da Tanzaniya.