SiyasaAfirka
Kenya ta sanar da makoki kan mutuwar hafsan kasar
April 19, 2024Talla
Shugaba Ruto ya sanar da zaman makoki ne domin nuna alhini da jimami kan mutuwar babban hafsan tsaron kasar Janar Francis Ogolla, sakamakon hadarin jirgi mai saukar Ungulu.
Karin bayani: Masu zanga-zanga shida sun mutu a Kenya
Jirgin na dauke da mutane 11 ciki har da Janar Ogolla, inda ya yi hadari a wani yanki da ke kusa da iyakar kasar da Uganda, acewar shugaba William Ruto.
Karin bayani: Ambaliya ta kashe mutane 70 a Kenya
Hafsan tsaron kasar na kan hanyarsa ce ta zuwa yankin arewacin kasar da ke fama da rikicin 'yan bindiga. Har ya zuwa wannan lokaci babu tabbacin musabbabin afkuwar hadarin jirgin.