1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiAfirka

Kenya za ta samu kudi daga asusun IMF

Suleiman Babayo MAB
April 30, 2024

Shugaban JKenya ya tabbatar da cewa asusu ba da lamuni na duniya IMF, zai bai wa kasar makuden kudin da take bukata domin zaburar da tattalin arzikin kasar da ke yankin gabashin Afirka.

https://p.dw.com/p/4fMS0
Shugaba William Ruto na Kenya
Shugaba William Ruto na KenyaHoto: Ihsaan Haffejee/AA/picture alliance

Shugaba William Ruto na kasar Kenya ya bayyana cewa asusun ba da lamuni na duniya, IMF, ya tabbatar da cewa kasar za ta samu kimani kudi dalar Amirka milyan dubu-daya a watan gobe na Mayu, lamarin da zai taimaka wajen inganta tattalin arzikin kasar da kaucewa shiga matsalolin rashin iya bashin da ake bin kasar cikin wannan shekara da muke ciki ta 2024.

Shugaba Ruto ya bayyana haka yayin taron da ke gudana a birnin Nairori fadar gwamnatin kasar ta Kenya tsakanin shugabannin kasashen Afirka da kuma hukumomin kudi na duniya.

Tun farko darajar kudin kasar ya farfado lokacin da gwamnati ta ba da jinkinar da kaddarorinta wajen tara kimanin kudin da ya kai dalar Amirka milyan dubu-daya da rabi cikin watan Febrairun da ya gabata. Ita dai Kenya ke kan gaba wajen karfin tattalin arziki tsakanin kasashen yankin gabashin Afirka.