1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kera na'urar adana bayanan asibiti a Gabon

Zulaiha Abubakar/GATSeptember 7, 2016

A kasar Gabon wani matashi dan shekaru 38 da haihuwa mai suna Fabrice Yonawah ya kirkiri na'urar adana bayanai tare inganta sadarwa a asibitocin kasar.

https://p.dw.com/p/1JwxZ
Ebola in Sierra Leone überwunden
Hoto: imago/Xinhua Afrika

A kasar Gabon wani matashi dan shekaru 38 da haihuwa mai suna Fabrice Yonawah da rasa aikin yi bayan kammala karatunsa na digirin-digirgir kan kimiyyar na'urar Computer a wata jami'ar kasar faransa, ya kirkiri wata na'ura wadda za ta adana bayanai tare kuma da sadarwa a asibitocin kasar .

Wannan na'ura da Fabrice Yonawah ya kirkira za ta adana duk wani bayanin lafiya na majinyaci, da zarar an shigar da bayanai a cikin na'urar ita kuma za ta adana a inda dukkanin likitoci da jami'an lafiya za su iya gani a cikin sauki. Wannan wani babbban cigaba ne ga bangaren lafiya a kasar saboda suna fama da matsalar adana bayanan marasa lafiya a asibitoci, kamar yadda likita Dr Artur Kanganga ya yi karin haske a lokacin da yake duba marasa lafiya tare da wannan na'ura.

DW Afrika Kodok Krankenhaus
Hoto: ICRC/Pawel Krzysiek

" In har akwai wata matsala, take sai mu taba inda aka yi alamar matsalar a jikin wannan na'ura, ba tare da mun koma mun dauko takardu mun yi binciken wacce takarda muke bukata don mu ga bayanin irin ciwon da ke damun majincyaci ba. Wannan kam wata hanya ce da za mu ba marar lafiya cikakkiyar kulawa".

Asibitin Dr Kanganga shi ne irinsa na farko da ya mayar da duk bayanan marasa lafiya da sadarwa a na'ura mai kwakwalwa hatta irin magungunan da likita zai rubuta wa marar lafiya da ranar da majinyaci zai dawo don sake ganin likita duk sun koma ta na'ura mai kwakwalwa. Wannan ta sa 'yan takardu kalilan ne suka rage a gurin ajiye bayanan marasa lafiya. Yonawah wanda ya kirkiri wannan na'ura ya yi wa shugaban asibitin bayanin cewa za a iya amfani da ita a kowanne bangare a cikin asibitin. An yi na'urar ne don ta hade bukatun asibitin guri daya in ji Fabrice Yonawah

" Mu a nan Afirka, bamu da intanet a kowanne asibiti, ko da yake a kan samu a wasu asibitocin, don haka lalle dole a nemi mafita yadda za a iya yin aiki ba intanet"

Iya cikin asibitin komai yana amfani da intanet,t o amma ana bukatar shi don tura bayanai ko karbar sakonni daga wasu asibitocin. Yonawah da sauran abokan aikinsa su 12, sun dauki fiye da shekaru biyar suna aiki don kirkirar wannan naura, sannan sun cigaba da ingantata don ta yi daidai da irin abin da ake bukata. Kirkirar wannan na'ura ta Yonawah ta lashe kimanin Euro1500.

Tunesien Sousse Terroranschlag
Hoto: Reuters/Z. Souissi

Kasar su Yonawah wanda ya kirkiri wannan na'ura watau kasar Gabon, kasa ce da take da arziki a cikin kasashen Afirka. Sai dai kashi uku na mutanen kasar suna fama da talauci. Wannan ce ta sa Fabrice Yonawah ya dawo gida bayan kammmala karatunsa a kan fasahar na'ura mai kwakwalwa a kasar Faransa, tare da kudirin kawo canji a kasar duk da cewar ya fuskanci matsaloli da yawa kafin mutane su fahimce shi.