Keta dokar tsarin zanga-zanga a Masar
November 29, 2013Masu zanga zangar sun ta rera wakokin neman ramuwar gayya a gangamin da suka yi wa taken "Daukar fansa na nan tafe". Burin da suka sa a gaba shi ne fafutukar neman ramuwar gayya kan wadanda ke da alhakin kisan gillan fursinoni kusan 40 da jami'an tsaro suka yi.
A unguwannin Giza da Hilwan da muhandessen dai, jami'an tsaro sunyi ta kokarin fasa zanga zangar da suka ce ana yinta ba tare da izini ba. a inda suka raunata mutane da dama tare da kame wasu. Amma dai daga baya, masu zanga zangar sun sake taruwa kana suka ci-gaba da jerin gwanonsu. Ko daya daga cikin masu zanga-zangar sai da ya ce "A biya mana bukatunmu na hukunta wadanda suka kashe mana 'yan uwa, idan ana so mu daina fita. Za mu ci-gaba da wannan gangami ba kakkautawa,har sai mun ga abin da ya turewa buzu nadi."
Dokar tsara zanga zanga wacce za ta kayyade adadi da wurare gami da lokacin yin zanga zanga,kana ta tanadi daukar matakan ladabtar da duk wanda ya karyata,ciki har da harbewa har lahira, ta jawo kakkausar suka ga gwamnatin da ita ma kanta ta samu isa kan mulki ne ta hanyar zanga zanga ga zabbabben shugaba. Lamarin da ya kai ga karuwar masu fito na fito da dokar. Na gaba-gaba daga cikinsu dai su ne matasan da suke hannun riga da kungiyar 'Yan Uwa Musulmi, yadda a yanzu suke neman hadewa don tinkarar abin da suka kira "harammataccen mulkin 'yan ina da kisa"."
A daura da haka,mahukunta da wasu 'yan kasar ta Masar na ganin cewa ya zama dole a halin yamutsin da kasar ke ciki a sanya dokar da za tarabe aya da tsakuwa.. Ko da shi ma wani mazaunin Alkahira cewa ya yi ""Idan muna son zaman lafiya, to dole ne mu mutunta kotuna da jami'a tsaro da sojoji domin wadannan su ne kashin bayan tsayuwar kasa"
Kamar dai yadda masu sa ido ke gani 'yan kasar za su dauki shekaru kafin kafa tsarin raba dai-dai, saboda sojojin ne suka mallaki kashi daya cikin uku na arzikin kasar. Sannan kuma jami'an tsaron kasar ta Masar sunsuka saba da karbar na goro..
Mawallafi: Mahmud Yaya Azare
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe.