Keta yarjejeniyar tsagaita wutar Ukraine
February 16, 2015Gwamnatin Ukraine da 'yan tawayen gabashin Ukarine masu samun goyon bayan Rasha sun zargi junansu da karya ka'idojin yarjejeniyar ta hanyar kaiwa junansu hare-hare. Haka nan kuma bangarorin biyu suna nuna adawa da kiran janye dukkanin manyan makamai dake yankin na gabacin Ukraine.
Mahukuntan Ukaine dai suka ce daga sanda yarjejeniyar ta fara aiki zuwa Litinin din nan (16.02.15) 'yan awaren da ke samun goyon bayan Rasha sun kashe sojin gwamnati biyar da kuma jikkata wasu da yawansu ya kai ashirin da biyar yayin da 'yan awaren suka zargi sojin gwamnati da kai farmaki a garururwan Luhansk da Donestk da suke iko da su.
Gabannin kaiwa ga wannan yanayi da ake ciki, masu sanya idanu kan rikicin na Ukraine da ma wanda ke shiga tsakanini sun yi dari-dari da samun irin wannan matsala. Wannan ne ma ya sanya ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Stineimer ya ce dorewar yarjejeniyar ta danganta ne da bin ka'idojin da ke cikinta sau da kafa musamman ma dai irin abubuwan da ake aiwatarwa a fagen daga.
To sai dai duk da wannan keta yarjejeniya da aka samu, masu shiga tsakani na cewar za su yi bakin kokarinsu wajen ganin an cimma nasarar da aka sanya a gaba amma kuma inji su tilas ne kowa ya gane cewar idan har aka kasa samun nasarar kokarin da ake ta yi a yanzu, to kuwa duk wanda wannan al'amari ya shafa musamman ma mazauna yankin na gabashin Ukraine za su dandana kudarsu.
A ranar Alhamis din da ta gabata ce dai aka kai ga cimma wannan yarjejeniya da ta fara aiki tsakar daren ranar Asabar din da ta gabata inda kunshin yarjejeniya ya tanadi jingine bude wuta da kuma janye makamai na yaki daga wuraren da aka ja daga.