1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Khashoggi: Trum ya musanta cewa yana kare Saudiyya

Salissou Boukari
October 18, 2018

Shugaban Amirka Donald Trump ya kare kansa daga zargin da ake yi masa na neman kare abokan huldarsa na kasar Saudiyya kan batun dan jaridar nan Jamal Khashoggi da ya yi batan dabo a Istanbul.

https://p.dw.com/p/36jky
USA Washington Saudischer Kronprinz Mohammed bin Salman bei Donald Trump
Hoto: picture-alliance/dpa/SPA

Da yake magana a gaban 'yan jarida a fadarsa ta White House, Shugaba Trump ya ce "ko kadan ba ya kare hukumomin Saudiyya, kawai dai ya na bukatar sanin gaskiyar lamari ne". Trump ya kara da cewa ya na jiran gaskiya ta bayyana ya zuwa karshen wannan makon duk kuwa da cewa kafofin sadarwa sun wallafa abubuwan da ke nunin cewa babu makawa an hallaka dan jaridar ne, wanda kuma ake zargin jami'an gwamnatin ta Saudiyya da suka fito daga birnin Ryad da hallaka shi.

Wannan lamari dai ya saka kasar ta Amirka cikin hali na tsaka mai wuya, ganin yadda take dasawa da kasar ta Saudiyya, inda kuma kowa yake jiran ya ga irin matakan da Amirkan za ta dauka a kai.