Saudi: Mutane 5 na fuskantar hukuncin kisa
November 15, 2018Sai dai kakakin ma'aikatar harkokin wajen Faransar ta ce, wajibi ne duniya ta ji cikakken bayani kan sakamakon binciken kisan wulakancin da aka yi wa dan jaridar, ba wai daga bangaren mai shigar karar Saudiyya kadai ba amma har daga sauran sassa daban daban da ke binciken lamarin.
Faransar dai na taka tsantsan da masarautar Saudiyyar tun bayan kisan Jamal Khashoggi, kasancewar shugaba Emmanuel Macron na muradin kulla dangantaka ta kut da kut da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman. Kazalika masarautar Saudiyya na daya daga cikin manyan masu cinikin kayayykin ma'aikatar tsaron Faransar.
A wannan Alhamis din ce dai babban mai gabatar da kara na masarautar ya sanar da hukuncin kisa kan 'yan kasar guda biyar da ake zargi da hannu a badakalar kisan gilla na wulakanci, sai dai sanarwar ta wanke Yarima Mohammed bin Salman.