1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mabiya cocin Kibdawan bakwai sun mutu a harin 'yan bindiga

Ramatu Garba Baba
November 2, 2018

Mutum 7 ne aka tabbatar da mutuwarsu wasu da dama suka sami rauni a yayin wani hari da 'yan bindiga suka kai kan wata mota kirar bas da mabiyan ke ciki a wannan Juma'a.

https://p.dw.com/p/37asr
Kairo Beerdigung der Toten des Terroranschlags auf eine koptische Kirche
Hoto: picture alliance/AP Photo/A. Nabil

Rahotannin na cewa, akwai mutane akalla bakwai da suka jikkata a sanadiyar harin. Tuni dai aka kaddamar da bincike da kuma farautar wadanda ke da hannu a harin. An kai harin kusa da wurin da aka kai wani hari makamancin na wannan rana a watan Mayu na shekarar 2017 da ya halaka Kibdawa ashirin da takwas.

Shugaban Masar Abdelfatah al-Sisi, a wani sakonsa bayan harin, ya jajantawa iyalan mamatan inda ya kuma sha alwashin ci gaba da yakar 'yan bindaga da suka buwayi kasar da ayyukan ta'addanci.