Kiir da Machar ne shirin kafa gwamnati
December 17, 2019Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da madugun 'yan tawayen kasar Riek Machar sun sha alwashin mutunta wa'adin kwanaki 100 da suka diba don kafa gwamnatin hadin kan kasa. Bayan wata ganawa da bangarorin biyu suka yi a wannan Talata, shugaban kiir ya ce sun cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin kan kasa kafin karshen watan fabrairu mai zuwa. Sai dai kuma a nasa bangare Riek Machar ya ce har yanzu ba su warware matsalar yawan jihohi da ya kamata Sudan ta Kudu ta kunsa ba.
Kasashen duniya sun jima suna nuna damuwa kan rikicin shugabanci da jaririyar kasar Sudan ta Kudu ta shafe shekaru tana fama da shi. An dai taba kafa gwamnatin hadin kan kasa tsakanin Salva Kiir da Riek Machar, amma kuma ba ta dore ba sakamakon sabanin da ke tsakanin bangarorin da ke hamayya da juna.