1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Killace ma'aikatan lafiya a Laberiya

September 29, 2014

Wata babbar jami'ar asibiti a Laberiya ta killace kanta da ma'aikatanta sakamakon cutar Ebola da ke saurin yaduwa da kuma lakume rayukan al'umma.

https://p.dw.com/p/1DNM5
Hoto: Zoom Dosso/AFP/Getty Images

Shugabar wani asibiti a Laberiya, Bernice Dahn ta killace kanta da ma'aikatanta bayan da mataimakiyarta ta mutu sakamakon cutar Ebola mai saurin kisa. Ministan yada labaran kasar Isaac Jackson ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce uwargida Dahn bata nuna wata alama ta cutar Ebola a jikinta ba. Ya kara da cewa Dahn ta dauki wannan matakin ne domin nuna da'a da kuma kwarewar aiki na ma'aikatan lafiya. Kasar Laberiya dai ta fi ko wacce kasa da cutar Ebola ta bulla yawan wadanda suka mutu sakamakon cutar da ma wadanda ke dauke da kwayar cutar ta Ebola. Kawo yanzu dai sama da rayuka 3,000 ne cutar ta lakume a kasashen yankin yammacin Afirka da annobar cutar Ebola ta afkawa.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu