Shugaban Koriya ta Arewa zai kai ziyara a Mosko
January 28, 2015Fadar Kremlin a ranar Larabannan ta bayyana cewa shugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jong-Un zai halarci bikin tunawa da yakin duniya na biyu da za a yi a birnin Moscow a watan Mayu mai zuwa a wani abu da ke nuna karon farko kenan da shugaban zai kai wata ziyara kasar waje tun bayan da ya hau kan karagar mulki a shekarar 2011.
Ziyarar shugaban na Koriya ta Arewa ta tabbata ana kuma shirye-shiryen tarbarsa a cewar mai magana da yawun shugaba Vladimir Putin na Rasha lokacin da ya ke bayani ga kamafanin dillancin labarin Interfex.
A cewar Dmitry Peskov mai maganar da yawun Shugaba Vladimir Putin shugaba Kim na daga cikin shugabannin kasashen duniya da aka gaiyyata dan halartar wannan gagarimin biki na tunawa da yakin duniyar na biyu.
Shi ma dai shugaban kasar Amirka Barack Obama na daga cikin wadanda aka gayyata wannan gagarimin bikin na tunawa da shekaru 70 da Tarayyar Sobiyat ta samu nasara kan dakarun Nazi na Jamus a lokacin yakin duniya na biyu.
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Pinado Abdu Waba