1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kim ya tantance inda zai kai hari a Koriya ta Kudu

Abdul-raheem Hassan
November 25, 2023

Shugaba Kim Jong Un ya tantance hotunan da sabon tauraron dan adam na leken asiri ya dauka, na manyan yankunan da yake shirin kai wa farmaki da makamai a cikin kasar Koriya ta Kudu.

https://p.dw.com/p/4ZR3f
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un da wasu dakarunsaHoto: KCNA/Reuters

Kafafen yada labaran kasar Pyanyong sun ruwaito cewa wuraren da tauraron dan adam ya hasko sun hada da Seoul babban birnin Koriya ta Kudu da sauran wuraren da sojojin Amirka ke da sansanoni.

A farkon makon nan ne Koriya ta Arewa ta sanar da harba tauraron dan adam na leken asiri na soji a sararin samaniya. Matakjin da ya haifar da shakku kan ganawar kaashen China da Japan da Seol din a karon farko tun 2019.

Sai dai manazarta a Koriya ta Kudu sun nuna shakku kan ikirarin gwamnatin Kim tare da cewa ya yi wuri a iya sanin ko tauraron dan adam - mai suna "Malligyong-1" yana aiki.