Kira da a sako Jamusawa a Iran
January 3, 2011Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da kanta ta fara wani yunƙuri do ganin an sako Jamusawan an biyu 'yan jarida da ake tsare da su a Iran. Kakakinta Christoph Steegman ya sanar da haka a birnin Berlin to amma bai yi ƙarin bayani game da takamamme irin ƙoƙari ko shirin da shugabar gwamnatin ke yi ba. To sai dai ya ce Merkel ta yi maraba da kiraye-kirayen da shugabannin siyasa da kuma wasu fitattun ƙasar suka yi na sako 'yan jaridar. A cikin jaridar Bild am Sonntag fitattun 'yan ƙasar su kimanin mutum 100 daga fannonin siyasa, tattalin arziki, al'adu da kuma wasannin motsa jiki sun yi kira ga Iran da ta sako ma'aikatan na jaridar Bild. Tun a cikin watan Oktoba aka kame mutanen saboda hira da suka so yi da ɗan wata mata da aka yankewa hukuncin kisa wato Sakineh Mohammed Ashtiani, ba tare da sun samu izinin aikin jarida a cikin Iran ba.
A wani taron manema labarai da ma'aikatar shari'ar Iran ta shirya, Sakineh Asthiani, ta nemi shigar da ƙarar 'yan jaridar ƙasar ta Jamus guda biyu da ake tsare da sun a ƙasar ta Iran.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas