Kiran da Merkel ta yi wa shugaban Kenya
July 12, 2011Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kira ga Kenya da ta ruɓanya matakan yaƙi da cin hacin da karɓar rashawa matiƙar ta na son 'yan kasuwan ƙetare da suka haɗa da na ƙsasarta su zuba jari a cikin ƙasar. Merkel ta yi amfani da ziyarar aiki da ta gudanar a kenya wajen yaba irin sauye sauye na siyasa da kuma na shari'a da ƙasar da ta fi ƙarfin tattalin arziki a gabashin nahiyar Afirka ta aiwatar a shekarun baya-bayannan. Sai dai ta ce sa ƙafar wando guda da cin hanci da karɓar rashawa ne, zai share hanyar haɓaka danganta a fannin tattalin arziki tsakanin Kenya da kuma Jamus.
"Ministocinsu sun sake tabbatar mana cewar za su tsaurara matakan yaki da cin hanci da karɓar rahswa. Muna da niyar haɓaka ƙawance na cinikayya tsakanin Kenya da Tarayyar Jamus. Amma kuma akwai bukatar ɗaukan matakan kare jarin da za a zuba."
Bayan ganawa da ta yi da shugaba Mwai Kibaki, shugabar ta gwamantin Jamus ta yi alƙawarin bayar da taimakon miliyon ɗaya na Euro domin a agaza wa 'yan gudun hijiran da ke tsugune a sansani mafi girma a duniya da ke kan iyakar Kenya da Somaliya. Baya ga ƙasar ta Kenya, Merkel za ta ya da zango a ƙasar Angola mai arzikin man fetur kafin, kafin ta nufi Tarayyar Najeriya inda batun makamashi zai mamaye ziyararta a birnin Abuja.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou