Kirsimeti: Fafaroma ya koka game da zubar da jini a Gaza
December 25, 2023Yayin da aka fara shagulgulan bikin Kirsimeti a duniya, jagoran Roman Katolika Fafaroma Francis ya koka game da tashe-tashen hankulan da ake ci gaba da fuskanta a duniya, inda ake ta zubar da jinin bil'adama a Gaza da Ukraine, a daidai lokacin da ake gudanar da gagarumin biki da ke alamta zaman lafiya.
Ya ce hatta garin da aka haifi Yesu Almasihu da ke Gabas ta Tsakiya an soke bikin, wanda ke karbar dubban baki da 'yan yawon bude ido domin shaida bikin, a don haka yake kira da a dakatar da yakin baki-daya, ba ma wai tsagaita wuta ba, kamar yadda ya yi jawabi a gaban dubban mabiya a fadarsa a daren Lahadi.
Karin bayani:Fafaroma Francis: Kananan yara cikin kunci
Da karefe 12 na Litinin din nan ne dai Fafaroma Francis zai yi jawabin sakonsa na bikin kirsimeti, da zai gabatar a fadarsa ta St Peter's da ke Vatican.
A Litinin din nan majalisar jagorantar yakin Isra'ila a Gaza za ta zauna domin tattauna batun bukatar dakatar da yakin, wanda kasar Masar ta nema, kamar yadda jaridar Jerusalem Post ta rawaito.
Karin bayani:Fafaroma ya yi kiran a samar da gajin jinkai a Zirin Gaza
A daren Lahadi ne dai jaridar Times of Isra'el ta rawaito cewa gwamnatin Isra'ila ta tabbatar da karbar wani sabon roko da Masar din ta yi ma ta, na shirin tsagaita wuta da musayar fursunoni, to amma an jiyo firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na nanata cewa yakin Gaza ba gudu ba ja da baya, har ya kammala kawar da duk wani burbushi na kungiyar Hamas.
Daga cikin kudurorin da Masar din ta shigar akwai tsagaita wuta ta tsawon makonni biyu, inda Hamas za ta sako Isra'ilawa 40 da ta yi garkuwa da su, yayin da Isra'ila za ta sako Falasdinawa 120. Sai kuma batun dakatar da yakin baki-daya, da sako dukkan fursunonin da ke hannun kowa, daga karshe Isra'ila ta janye sojojinta kana kuma Falasdinawan da suka bar muhallansu su koma gida.
Kamar yadda gidan talabijin din kasar Saudi Arebiya Asharq News ya rawaito.