Lafiya Jari: Me ke sa cuta ke bijire wa magani?
May 3, 2019Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi hasashen cewar mutane kamar dubu 435 suka mutu da ciwon zazzabin cizon sauro a shekara ta 2017. Galibi an sami mutuwar ne kuwa a cikin kasashen da ke kudu da hamada Dakta Usman Sadik Yelwa likita daga tarrayar Najeriya ya jadada cewar shekarun baya-bayan nan cutar na dada karuwa.
Canji na yanayi da sauran canje-canje na zamantakewar al‘umma ya sa sauron ya yi karfi sannan kuma ya kan yi dogon zango a cewar Dakta Usman Sadik Yelwa.
Akwai dubaru daban-daban da ake yin amfani da su na yaki da cizon sauron kamar su gidan sauro da ake rararabawa ga mata masu juna biyu da kuma yin tsabata. Ana dai shirin bullo da sabbbin magungunan na yaki da ciwon sauro baya ga wadanda ma ke yin tasiri.
To sai dai sauron ya kan bijirewa magungunan ana sha kamar ba a sha, cutar na ci gaba da kasancewa shin ko menene dalili Dakta Ibrahim Abdullahi likita ne daga Najeriya ya ce yawancin kwayoyin cutar kan canza kama yadda maganin baya gane su, ko su buya. Haka nan rashin bin ka’idoji na shan magani na sanyawa a gaza warkewa.