Ko Steinbrück zai iya kada Merkel?
September 11, 2013Ɗan takaran jam'iyyar Social Demokrat na shugaban gwamnatin Jamus a zaɓe da ke tafe, ana yi masa kallon wani mai basira kana kwararre a harkar tattalin kuɗi. Duk da cewa ra'ayoyin masu zaɓe da aka fitar kawo yanzu suna nuna cewa Steinbrück yana da matsala, amma ɗan takaran yana ganin zai iya samun nasarar zaɓen.
Ɗan shekaru 66 da haifuwa da ke yi wa jam'iyyar SPD takaran muƙamin shugaban gwamantin Jamus, Peer Steinbrück tuni ya fara jawabai tamkar wanda yake ganin ba makawa zai ɗare kujerar shugabancin gwamnati.
"Zan kasance shugaban gwamnatin Tarayyar Jamus"
Steinbrück dai ɗa ne ga wanin iyalin 'yan kasuwa da ke birnin Hamburg, ya kuma yi shekaru yana taka rawa a jam'iyar Social Demokrat. Inda ya riƙe muƙaman siyasa daban daban. Bayan kammala karatun jami'a inda ya karanci tattalin arzikin ƙasa, ya fara aikinsa ofishin shugaban gwamnatin Tarayyaar Jamus, da ga bisa ni ya yi ɗan majalisar dokiki, ya kuma riƙi muƙamin ministan kuɗi, kana ya taɓa kasancewa gwamnan jihar Nordrhein Westfaliya. Inda a lokacin yana ministan kuɗi shi da Angela Merkel, tare suka yi famar dai-daita tattalin arzikin ƙasar. Ga ma a yanzu abinda yake faɗi kan shugabar kana abokiyar fafatawarsa Angela Merkel.
"Ta dai taimaka ne kawai, amma ba ita ce ta tsara ba, aksarin shirin ceto tattalin arzikin ƙasa da muka yi. Tsari ne na jam'iyyar SPD"
Shi dai Peer Steinbrück na ɗaukar kansa a matsayin wanda ya fara kana ya tsara ceto tattalin arzikin Jamus, amma akwai fa wasu matsalolin. Domin kafin a bara da jam'iyyar SPD ta zai da shi ɗan takara, ya samu ɗimbin kuɗi a matsayinsa na ɗan majalisar dokoki dake kula da harkar bankuna.
Don haka 'yan ƙasar da dama na aza ayar tambaya, shin mutumin da a lokacin da yake kula da harkar bakuna a majalisar dokoki ya tara ɗimbin kuɗi, shin a yanzu idan aka zaɓe shi shugaban gwamnati mi zai yi wa jama'a. Amma Steinbrück wanda ke da matuƙar basira tuni ya juya hankulan jama'a yana cewa, in dai aka zaɓe shi, to zai sa hamshaƙai su riƙa biyan haraji mai tsoka, domin a dai-daita ruwayar al'ummar Jamus.
"A shekarun baya mun fiskanci matsalolin kamfanoni masu zaman kansu, inda hamshaƙai ke ƙara arzurta kansu, sauran talakawa kuwa suna ƙara talaucewa. Wannan ba shine manufar ta, ko ta jam'iyya ta ba. Don haka abinda zan sa a gaba shine, inganta rayaƙasa, ilimi, rage yawan basukan da ke kan ƙasarmu, ƙarfafa jama'a, wannan ita ce manufa ta"
Steinbrück na da manufar dai-daita 'yan ƙasa ta fannin albashi, zai kuma mayar da hankali kan hauhawar farashin kaya, kana zai ƙarfafa yancin mata a wuraren aiki.
"Ina wakiltar tsarin tattalin arziki, irin na Gerhard Schröder ne, wato tsohon shugaban gwamnatin Jamus a jam'iyyar SPD. Wannan shine dalilin da ya sa har yanzu ƙasarmu ke da tattalin arziki mai inganci. Na son cewa akwai matsalolin har yanzu da ake fiskanta, yakamata mu samar da ƙarin guraben aiki, wannan itace manufa ta"
A batun harkokin waje dai, Steinbrück na mai son a mutunta yancin Jamus, musamman bisa tsarin Amirka na sauraro da naɗar bayanan sadarwa. Kana yana mai ra'ayin san'y'ya Tukiya cikin ƙungiyar Tarayyar Turai. Ƙasarshen gabacin Turai mataulata kuwa, a manufar sa dole a sauƙaka musu basukan da ake binsu.
Mawallafa: Wolfgang Dick / Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu