NSU-Prozess ohne türkische Medien?
March 27, 2013Kafofin watsa labaran Turkiya na ci gaba da tsokaci dangane da rashin basu damar shaidar da shari'ar wasu jamusawa 'yan Nazi da suka kashe wasu 'yan kasarsu takwas shekaru shidan da suka gabata. Ranar 17 ga watan Afrilu ne wasu masu kyamar launin fata hudu za su hallara gaban kotun birnin Munich domin kare kansu daga tuhumar da ake yi musu.Mohammed auwal Balarabe na dauke da karinn bayani.Ita dai kotun birnin Münich ta na tuhumar Beate Zschäpe da kuma wasu 'yayan kungiyar nazi ta NSU hudu da marar hannu a kisar da aka yi wa wasu 'yan Turkiya takwas da kuma wani dan Girka daya tsakanin shekaru 2000 zuwa 2006. Tun a watan Nowamba 2011 ne aka danketa, a daidai lokacin da ake tsaka da muhawara kan wajibcin haramta jam'iyar NPD da ke da ra'ayin 'yan Nazi koko a'a.
Sai dai kuma gabanin shari'ar da za a fara a ranar 17 ga watan Afirilu mai zuwa, kotun ta fitar da sunayen kafofin watsa labarai hamsin da ta bai wa izinin shaidar da yadda shari'ar za ta gudana. Babban abin da ya dauki hankali shi ne rashin sunan kafar watsa labaran Turkiya ko da daya ne a cikin jerin wadanda aka ba wa izini, duk shafarta da shari'ar ta yi kai tsaye. Alal hakika ma dai dimbin 'yan asalin Turkiya da suka shafe shekaru da dama a Jamus, suna ci gaba da kallon tasoshin telebijin na kasarsu ta asali. Saboda haka ne Mustafa Görkem wani dan jarida na Turkiya ya ce wannan matsayi na kotun Jamus bai dace ba.
"Abu ne mahimmaci mutun ya san halin da sassan biyu ke ciki:wato Matsayin Jamus da kuma ra'ayin Turkawa game da wannan batu. 'Yan asalin Turkiya sun shafe shekaru 50 zuwa 60 suna rayuwa a Jamus. Amma wannan shi ne karon farko da suka fuskanci wariya. Wannan ne ya sa suke daukar shari'ar da mahimmaci. saboda haka ne ba su ji dadin wannan al'amari ba."
Yawan kafofin labarai da ba su samu izini ba
Baya ga kafofin watsa labaran Turkiya, su ma na kasashen waje wadanda suka hada da BBC da Aljazeera da New-York Times ba su sami izinin shaidar da shari'ar ba. Ita dai kotun birnin Münich ta ce ta bayar da izinin ga kafofin watsa labarai hamsin da suka fara mika mata bukata. Sai dai tuni jaridar Jamus da ake bugawa a kulli yaumin wato Bild ta yi tayin gurbinta ga takwararta ta Turkiya Hürryiyet . Amma dai Eva Werner da ke magana da yawun hadeddiyar kungiyoyin kara hakkin 'yan jarida a Jamus DJV a takaice, ta ce kamata ya yi a samarwa kafofin watsa labaran Turkiya da kuma na ketare gurbi a zauren sauraran shari'ar.
"Mu a hadeddiyar kungiyar DJV da ke kare 'yancin 'yan jarida muna ganin cewar bai dace a ce 'yan jarida 50 ne kawai za su halarcin zaman na kotu ba. Inda gizo ke saka ma shi ne rashin bai wa kafofin watsa labaran Turkiya da kuma na kasashen wajen damar shaidar da yadda shari'ar za ta gudana. wannan tsari ne da ba zai daga darajar bangaren shari'a a Jamus ba."
Su dai kafafin watsa labaran ketare su na so ne su shaidar da kamun ludayin Jamus game da kashe kashe na wariyar launin fata da ya shafa mata kashin kaji a baya.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar