Kofi Annan zai yi jawabi akan yunkurinsa na sulhunta rikicin Siriya
March 16, 2012A yau ne tsohon sakataren Majlisar Dinkin Duniya Kofi Annan kuma manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniyar da kungiyar kasashen larabawa akan rikicin Siriya zai yiwa kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniyar jawabi ta Video game da yunkurin sulhunta rikicin na Siriya. Jakadu a Majalisar Dinkin Duniyar sun ce nazarin da Kofi Annan din ya yi na halin da ake ciki zai kasance mai matukar muhimmanci ga Amirka da kawanyenta na tarayyar Turai wajen zartar da wani daftarin kudiri da zai tabbatar da baiwa jami'an agaji damar shiga garuruwan da sojojin gwamnatin Siriyan suka yiwa kawanya. Sau biyu kasashen Rasha da China suna hawa kujerar na ki akan kudirin yin Allah wadai da gwamnatin Siriyar.
A dai halin da ake ciki tattaunawa tsakanin kasashen nan biyar masu kujerar dundundun a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniyar da kasar Morocco akan wani sabon daftarin kudiri ta ci tura sai dai kuma ana sa ran cigaba da tattaunawar bayan Kofi Annan ya yiwa kwamitin sulhun jawabi. Tun da farko Kofi Annan bayan da ya gana da mahukuntan Siriya a Damascus da kuma bangaren yan adawa a birnin Ankara na kasar Turkiya yace wajibi ne gwamnati da yan tawayen Siriya su sanya muradun al'ummar siriya akan gaba domin kawo karshen rikicin.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi