1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta fita daga gasar cin kofin duniya

Abdullahi Tanko Bala
June 27, 2018

A fafatawar da aka yi a cigaba da gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya Koriya ta Kudu ta doke Jamus da ci 2-0 a karawar da suka yi da yammacin wannan rana ta Laraba.

https://p.dw.com/p/30PPb
FIFA Fußball-WM 2018 in Russland | Deutschland vs. Südkorea
Hoto: Reuters/D. Martinez

A karon farko a tarihin kwallon kafa na duniya an fidda Jamus a zagayen farko na gasar.

Tarihi ya nuna rabon da a kori Jamus a irin wannan yanayi tun a shekarar 1938.

A fafatawar da suka yi da yammacin wannan rana ta Laraba, Koriya ta Kudu ta lallasa Jamus da ci 2-0 abin da ke zama mummunan koma baya ga kungiyar kwallon kafar ta Jamus.

Jamus wadda ita ce ke rike da kofin a yanzu ta sami nasarar daukar kofin kwallon kafar na duniya har sau hudu a baya.

Sai dai duk da nasarar da Koriya ta Kudu ta samu ba za ta iya wucewa zuwa zagaye na gaba ba.

A sakon da ya wallafa a shafin Twitter mai magana da yawun shugabar gwamnati Jamus Angela Merkel ya baiyana kaduwa yana mai baiyana sakamakon da cewa abin takaici ne ga kasar baki daya.

Mai horar da yan wasan na Jamus Joachim Loew yace zai dauki lokaci domin nazarin matsayinsa bayan shan kaye da kungiyarsa ta yi.

A halin da ake ciki kuma kuma Sweden da ci Mexico 3-0 wanda ya basu damar wucewa zuwa zagaye na gaba na kungiyoyi 16.