Kokarin bunkasa tattalin arzikin Afirka
May 10, 2022A kasashen Afirka kudu da Sahara akasari batun yawon bude ido da shakatawa ba sa samun kulawa ta musamman, yayin da a wasu kasashen harkar ta baki masu yawon shakatawa ko yawon bude ido ke zama babbar harkar habbaka tattalin arziki. Masanan sun bayyana cewa idan ana son ceto harkar yawon shakatawa a Afirka, ya zama dole gwamnatoci su rika sassauta kudaden shiga na irin wadannan wuraren ga 'yan asalin kasashensu.
Kasashen Gabashin Afirka suna babban misali a harkar yawon shakatawa, Kenya da Zambiya da Zimbabuwe. Kogin Sambesi da ke kan iyakar Zambiya da Zimbabuwe da Viktoriya fall a Zimbabuwen wanda ke da zurfin mita kimanin 110 irin wadannan da sauransu duk abubuwa ne da baki ke matukar sha’awar gani, amma kuma 'yan asalin kasashen ba su cika zuwa ba, ba don komai sai yadda gwamnatoci ke tsauwala kudaden shiga don ganin irin wadannan wuraren da Allah ya horewa kasashen.
Wannan yanamatukar shafar ma'aikacin yawon shakatawa Wandanda ke harkar tsara tafiyar baki. Hakan kuwa shi ne babban dalilin da yasa a kasashe masu tasowa na Afirka ba a cika bada mahimmanci domin kai ziyara wuraren shakatawa ko yawon bude ido ba.
Ga wasu na cewa babbar matsalar da ke shafar yawon shakatawa a Afirka, kusan ba a bada fifiko ga ‘yan kasa a kan baki, kai hasali ma an fi kula da baki daga kasashen waje musamman ma Turawa, yayin da su kuwa 'yan kasa ke ganin wannan ba shi ne babbar matsalarsu ta rayuwa, domin ga tsadar shiga wuraren shakatawa ga kuma matsalolin tattalin arziki.
Annonabr corona ta yi matukar kassara harkar yawon bude ido, misali kasar Afirka ta Kudu a shekara daya gabanin corona sun samu baki kimanin miliyan goma daga 'yan yawon bude ido amma idan aka kwatanta da bara, masu yawon bude ido ba su fi miliyan biyu da dari biyu ba. Kasar Kenya ta yi matukar sausauta kudin shiga wuraren yawon bude ido, yayin da ita kuwa kasar Ruwanda dama can ta jima da bambanta kudin shiga wuararen shakatawa a tsakanin baki da 'yan kasa.