1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunusiya:Ceto bakin haure a gabar teku

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 25, 2022

Masu aikin ceto a Tunusiya na ci gaba da laluben mutane da dama da suka bace, bayan da nutsewar wani kwale-kwale makare da bakin haure.

https://p.dw.com/p/4BsJw
Ceton bakin haure a ruwa
Da ma dai bakin hauren sun saba yin kasada da rayuwarsu a kwale-kwale marar inganciHoto: Ahmed Hatem/AP Photo/picture alliance

Rahotanni sun nunar da cewa bakin hauren da suka fito daga Libiya, na kokarin tsallakawa Turai ne da suke yi wa kallon tudun mun tsira. Kwale-kwalen dai, ya nutse ne a gabar ruwan Tunusiyan. Hukumar Kula da Kaurar Jama'a ta Kasa da Kasa ta bayyana cewa an ceto mutane 30 yayin da wasu 75 suka yi batan dabo kana an gano gawar mutum guda, bayan da kwale-kwalen da suke cikin ya nutse a birnin Sfax da ke kudancin Tunisiya. Da yake karin haske kan batun maimagana da yawun mahukunta a birnin na Sfax Mourad Turki ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na  Associated Press cewa, mutanen da aka ceto shekarunsu sun kama ne daga 18 zuwa 40 a duniya. Mutanen dai sun hada da 'yan kasashen Bangaladash da Masar da Maroko da kuma Kamaru.