1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin girka dimokaradiyya a Afirka ta Tsakiya

Yusuf BalaDecember 30, 2015

Zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki zai bude kofar samun zaman lafiya da girka dimokaradiyya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/1HWBB
Afrika Wahlen in Zentralafrika
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Zaben da tun da fari aka tsara yin shi a watan Oktoba na cike da rashin tabbas. Ga dai matsalar tsaro inda aka jibge dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dubu 10 da dakarun Faransa 900 da ake kira Sangaris a birnin Bangui da ke zama matattarar rikici. Ga kuma matsalar lokaci ganin an kai takardun kada kuri'ar a ranar Litinin ne birnin na Bangui kwanaki biyu kafin zaben. Ko da yake masu kada kuri'a miliyan biyu sun yi rijista ba lallai ba ne kowa ya samu damar yin zabe. Abin da wasu masanan ke ganin an girka shirin zaben ne bisa ginshiki mara kwari. Roland Marchal mai bincike ne a cibiyar nazarin siyasa a Paris ya yi karin haske.

"Banda jami'an diplomasiyya an hakikance cewa ranar da za ta biyo bayan zabe na da muhimmanci fiye da ranar da za ta kasance kafin ranar zabe.

Sabbin hukumomi za su gaji tarin matsaloli

Sabuwar gwamnati dai da ake fata za ta gaji tulin kalubale ganin yadda kowane bangare na addinan biyu da suka fi karfi a kasar ya fusata, ga 'yan tawaye dauke da makamai, ga yadda za a samu a dawo da mutanen da suka yi wa kasar kaura su dubu 450 zuwa dubu 460 da suka watsu a cikin kasar.

Afrika Wahlen in Zentralafrika
Tun da sanyin safiya masu zabe suka yi dogon layi don sauke wannan nauyiHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Babu dai tabbaci ko zaben na wannan Larabar zai iya kai labari ba tare da katsalandan ba na rikicin addini ganin har yanzu wasu yankunan na hannun 'yan tawayen. A nan ma ga abin da Roland Marchal ke cewa.

"Alamu na nuna cewa akwai yiwuwar tashin hankali ya barke, ko da kuwa ba a nan kusa ba cikin watanni shida da ke tafe lokacin da hankulan al'ummomin kasa da kasa ya kau daga kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, lokacin da kowa ya tafi da tunanin cewa an kammala zabe lafiya a kasar."

Tallafi daga duniya zai taka rawar gani

Kasar dai ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na bukatar tallafin kasa da kasa dan kada ta kai ga durkushewa a cewar Charles Malinas jakadan Faransa a birnin na Bangui.

Afrika Wahlen in Zentralafrika
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

"Al'ummar kasa da kasa za ta ci gaba da sa ido kan wannan kasar. Majalisar Dinkin Duniya na nan, haka nan kuma Faransa na tallafa mata a wannan lokaci da take tsaka mai wuya, babu yadda za a yi a watsar da al'ummar wannan kasa ta Afirka ta Tsakiya."

'Yan takara 30 ne dai ke neman shugabancin kasar ciki har da Anicet-Georges Dologuele, tsohon Firaminista da Martin Ziguele, wanda daga cikinsu ake sa rai ya iya samun kuri'un da za su kai shi zagaye na biyu na zaben. Sai kuma Karim Meckassoua, da ke zama tshohon minista daya kuma daga cikin 'yan takara biyu Musulmai.