1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Allurar rigakafin cutar Maleriya ta karbu a kasashen EU.

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 24, 2015

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta amince da sahihancin allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro wato Maleriya ta farko a duniya.

https://p.dw.com/p/1G4Ft
Yara kanana masu yawa na mutuwa sakamakon Maleriya
Yara kanana masu yawa na mutuwa sakamakon MaleriyaHoto: AP

Kungiyar ta EU ta ce allurar na da sahihancin gaske kuma za a iya yiwa jarirai a nahiyar Afirka amfani da ita ba tare da sun sami wata illa ba. Allurar mai suna Mosquirix kamfanin sarrafa magunguna na GlaxoSmithKline da kuma shirin PATH Malaria Vaccine ne suka samar da shi kana zai iya kare dinbin al'umma daga kamuwa da cutar da ita ma ke saurin kisa a Afirka. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce za ta tantance ingancin allurar rikagafin ta Mosquirix wadda ake wa lakabi da RTS,S da wani bangare na tallafin samar da ita ke fito daga gidauniyar Bill & Melinda Gates domin tabbatar da sahihancinta cikin watan Oktoba mai zuwa, kana ta bayar da damar yin amfanin da ita a nahiyar Afirka cikin watan Nuwamba na wannan shekara. Cutar Maleriya dai na daya daga cikin manyan cutukan da suka fi hallaka kananan yara musamman ma a yankin Kudu da Saharar Afirka inda take daukar rayuwar yaro daya duk cikin minti guda, kana a duk shekara mutane miliyan 200 ke kamuwa da ita.