Kokarin samar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya
November 28, 2006Faraministan Israela, Ehud Olmert yace kasar sa a shirye take ta koma teburin sulhu da Palasdinawa, don kawo karshen dauki ba dadin dake wanzuwa a tsakanin su.
Mr Olmert ya kara da cewa Israela a shirye take ta sadaukar da wasu yankuna nata ga Palasdinawa, a kokarin da ake na ganin an samu zaman lafiya.
Bugu da kari faraministan na Israela ya tabbatar da cewa nan bada dadewa ba Israela zata sako da yawa daga cikin Palasdinawa fursunoni da take tsare dasu, a matsayin musaya na sojin kasar guda da aka sako.
Idan dai an iya tunawa garkuwa da sojin na Israela, wato Gilad shalit a watan junin daya gabata, ya haifar da mugun dauki ba dadi a tsakanin bangarorin biyu.
Duk dai da yarjejeniyar tsagaitawa da bude wuta da aka cimma a tsakanin bangarorin biyu, har yanzu ana fuskantar barazanar kai hare hare a tsakanin juna.