Taron sasanta rikicin Falasdinu da Isra'ila
June 3, 2016Ko da yake taron na wakanan ne ba tare da wakilan bangarorin da batun ya shafa ba wato Isra'ila da Palasdinu, sai dai Faransa wadda ta dauki bakuncin taron na kasa da kasa a birnin Paris da ya hada ministocin harkokin wajen manyan kasashen duniya 25 gami da sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon, ta ce ya kamata a kira wani babban taron zaman lafiya na kasa da kasa da za a saka Isra'ila da Falasdinu a ciki kafin karshen wannan shekara. Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Marc Ayrault ne ya nunar da haka a sanarwar bayan babban taron sake farfado da zaman lafiyar.
Kokarin da aka yi na farko na shawo kan Isra'ila da Palasdinu su cimma wata yarjejeniya duk sun ci-tura. Falasdinawa na cewa fadada unguwannin 'yan share wuri zauna da Isra'ila ke yi a yankunan da ta mamaye na dakushe fatansu na samun kasarsu a yankin Gabar Yammacin da Kogin Jordan da Zirin Gaza da kuma Birnin Kudus.
Zargin juna a tsakanin bangarorin biyu
Ita kuma a nata bangaren Isra'ila na bukatar Falasdinawa su dauki tsauraran matakan tsaro sannan su murkushe sojojin sa-kai da ke yawaita kai hare-hare kan fararen hular Isra'ila. Ita ma Isra'ila ta ce Birnin Kudus shi ne babban birninta, ba za ta iya rabawa da Falasdinawa ba yayin da suma a hannun guda Falasdinawan ke son a bar musu birnin Kudus din domin ya zama babban birninsu.
Shin za a iya samun mafita ke nan kasancewa kowane bangare ya tsaya daram kan bakarsa? Avi Primor shi ne tsohon jakadan Isra'ila a Jamus ya ce abin da kamar da wuya wai gurguwa da auren nesa. Dangane da wannan rashin hangen mafita daga rikicin tsakanin Isra'ila da Palasdinu ya sa mahalarta taron na birnin Paris, a wannan Jumma'a suka bukaci da a gaggauta hada karfi da karfe don cimma tudun dafawa.
Bukatar tabbatar da yin taron sulhu
Sanarwar bayan taron dai ta jaddada bukatar samar da masahala tsakanin bangarorin biyu biyu da ma tattauna kai tsaye a tsakaninsu bisa tanade-tanaden kudurorin Majalisar Dinkin Duniya.