Rikicin Burundi na ci gaba da daukar hankali
November 11, 2015Wani jami'in kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa akwai yi wuwar majalisar ta yi gaggaawar tura dakarun wanzar da zaman lafiya na MONUSCO da ke makwabciyar Burundin wato Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango domin kaucewa afkuwar irin kisan kiyashin da ya taba faruwa a Ruwanda, in har al'amura suka ci gaba da tabarbarewa a Burundin. Ya kara da cewa rundunar ta MONUSCO da ke da dakaru 20,000, ka iya samun karin kwarrarun sojoji da ga Afirka ta Kudu da Tanzaniya da kuma Malawi. Kasar Burundi dai ta samu kanta cikin halin kunci da ya hadar da azabtarwa da kisa da kuma tsare mutane ba bisa ka'ida ba, tun bayan da Shugaba Pierre Nkurunziza ya kaddamar da shirinsa na yin tazarce a watan Afrilun da ya gabata wanda kuma ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar .