1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin shawo kan rikicin yankin gabas ta tsakiya

February 18, 2007
https://p.dw.com/p/BuRW

Gabannin taron kolin kusurwa uku, Sakatariyar harkokin wajen Amurka CR, zata tattauna a wawware da faraministan Israela Mr Olmert da kuma takwaran sa na palasdinu ,Mahmud Abbas.

Wannan tattaunawa dai a cewar rahotanni, na a matsayin share fagen taron kolin kusarwa uku ne na yunkurin kawo karshen rikicin YGT.

Taron kusurwa ukun dai ana sa ran zai wanzu ne a gobe litinin a tsakanin CR da kuma mahukuntan Israela da yankin palasdinu.

A cikin bayanin ta a lokacin taron manema labarai, CR ta tabbatar da muhimmancin wannan taro, musanmamma don samo bakin zaren rikicin dake tsakanin Palasdinawa da Israela.