Kokarin warware rikicin Yankin Gabas ta Tsakiya
November 21, 2007Amirka ta ce shirye shirye sun yi nisa game da gudanar da taron kolin Yankin Gabas ta Tsakiya.Mahukuntan na Amirka sun tabbatar da cewa, a mako mai zuwa ne ake sa ran gudanar da taron, a jihar Maryland dake ƙasar. A yanzu haka ma dai a cewar Amirka tuni aka aike da takardun gayyata ga Israela da Falasɗinawa, a hannu ɗaya kuma da Majalisar ɗinkin duniya. Haka kuma an aike da gayyatar ga ƙasashen Saudiya da kuma Syria. Amirka a yanzu na ƙokarin janyo hankulan ragowar ƙasashen na larabawa aikewa da wakilinsu ga wannan taro. Kafin dai gudanar da taron ana sa ran shugaba Bush zai gana da Faraministan Israela Ehud Olmert da takwaransa na Falasɗinawa Mahmud Abbas. Rahotanni dai sun shaidar da cewa wannan taro na a matsayin irinsa na farko, a tun bayan shekara ta 2000 da ta gabata.