An nemi Isra'ila da Hesbollah su tsagaita wuta a Lebanon
September 26, 2024Amurka da Faransa da Kungiyar Tarayyar Turai da wasu kasashen Labarawa sun bukaci a tsagaita wuta take-yanke na tsawon kwanaki 21 a Lebanon inda rikici ke kara kamari tsakanin Isra'ila da kungiyar Hesbollah tare da barazanar yaduwa a yankin Gabas ta Tsakiya. A cikin sanarwar hadin gwiwa da kasashen suka fidda ciki har da Jamus, sun ce suna son a mayar da hankali kan tattaunawa domin kawo karshen zubar da jini a wannan iyaka ta Isra'ila da Lebanon da kuma Zirin Gaza.
Karin bayani: Fargabar yaki tsakanin Isra'ila da Lebanon
Shugaba Joe Biden na Amurka da takwaransa Emmanuel Macron na Faransa sun ce suna aiki tukuru domin ganin an warware wannan rikici ta hanyar diflomasiyya bayan wata ganawa da suka yi a daura da taron Majalisar Dinkin Duniya na birnin New York. Sai dai wadannan shugabannin kasashe sun yi fatan samun cikakken hadin kan gwamnatocin Isra'ila da Lebanon don amincewa da wannan tayi.