1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka: 'Yancin aikin jarida na fuskantar koma baya

Sakpa Delali GAT/MNA
January 9, 2020

Waiwaye kan yanayin aikin jarida a kasashen Afirka a shekarar da ta gabata da kuma halin da ake ciki a farkon wannan shekara ta 2020.

https://p.dw.com/p/3VwWl
Afrika Pressefreiheit l Uganda - Protest für Pressefreiheit - Daily Monitor Zeitung
Hoto: Getty Images/AFP/M. Sibiloni

Aikin jarida ya zamo babban jidali da hadari ga 'yan jarida a kasashen Afirka na Kudu ga Sahara a shekara ta 2019 inda 'yan jarida da dama suka tsinci kansu a gidan kurkuku ko kuma cin zarafinsu a sakamakon aikinsu. Akasarin 'yan jaridar dai an tsare su ne a bisa zargi dabam-dabam, a mafi yawancin lokuta a bisa zargin aikata laifukan da ba su taka kara sun karya ba, ko kuma a bisa zargin da ba shi da tushe balantana makama.

Kungiyar kare 'yancin aikin jarida ta kasa da kasa ta Reporters sans Frontieres ta bayar da misalai masu yawa a rahotonta na shekara ta 2019, inda alal misali a watan Oktoba mahukuntan kasar Burundi suka kame wasu 'yan jarida guda hudu na jaridar Iwacu da ke zama daya daga cikin kwarorin jaridu masu zaman kansu a kasar.

Mahukuntan Burundin sun zargi 'yan jaridar da cin amanar kasa bayan da suka kama su sun je hada rahoto kan wani farmaki da kungiyar 'yan tawayen Burundi a gabashin Kwango Kinshasa suka kawo a Arewa maso Yammacin kasar. Dama dai yau shekaru uku da aka daina jin duriyar Jean Bigirimana da ke yi wa jaridar ta Iwacu aiki, bayan da jami'an leken asirin gwamnatin Burundi suka sace shi. Antoine Kabuhare editan jaridar ta Iwacu ya yi karin bayani kan hadarin da ke tattare da aikin jarida a Afirka yana mai cewa:

'Yan jarida kamar nan a Burundi sun sha yin zanga-zangar neman 'yanci kan aikinsu
'Yan jarida kamar nan a Burundi sun sha yin zanga-zangar neman 'yanci kan aikinsuHoto: Esdras Ndikumana/AFP/Getty Images

"A kasashenmu akwai gwamnatocin da ke kyamar aikin jarida, domin ba sa son ana fallasa labarai munanan halayensu kamar na cin hanci da azabtar da fararan hula."

A kasar Kamaru ma duk kanwar ja ce, inda 'yan jarida ke dandana kudarsu a hannun gwamnatin Yaounde wacce ta kame tare da kargame Christophe Bobiokono editan jaridar Kalara, wacce da ta yi fice a binciken kwa-kwaf musamman a fannonin harkokin shari'a a kasar. Haka zalika a kasar Chadi inda mahukuntan suka kame Martin Inoua Doulguet editan jaridar Salam Info. Dukkan 'yan jaridun biyu an tsare su ne a bisa zargin aikata laifukan da ba su taka kara sun karya ba.

'Yan jarida masu daukar hoto ma na fuskantar tarnaki wajen gudanar da aikinsu
'Yan jarida masu daukar hoto ma na fuskantar tarnaki wajen gudanar da aikinsuHoto: picture-alliance/dpa/W. Kumm

Dama dai yau shekaru uku kenan da mahukuntan kasar Kamaru ke tsare da Amadou Vamoulke tsohon editan gidan rediyo da telebijin na kasa na CRTV a babban gidan kurkuku na birnin Yaounde. A kan haka ne Arnaud Frogger na ofishin kungiyar Reporters sans Frontieres reshen Afirka ya ce ya kamata a ci gaba da matsa kaimi ga mahukunta a kasashen da ake tsare da 'yan jarida domin ganin an sako su.

"Babu dalilin da zai sa a tsare dan jarida a tsawon makonni, watanni ko ma shekaru a gidajen kurkuku a bisa laifin kuskuren alkalami a cikin aikinsu. Wannan kira ne ga shugabannin kasashen Afirka renon Faransa, domin ganin sun sauya hali da ba da hadin kai ga kawo karshen kame-kamen 'yan jarida."

Babban fatan da ake da shi dai a wannan shekara ta 2020, shi ne na kawo karshen kame-kamen 'yan jarida a kasashen Afirka da sakin wadanda ake tsare da su a gidajen kurkuku, da kuma fatan suma 'yan jaridar musamman wadanda ke bata rawar sauran takwarorinsu da tsalle, za su gyara halinsu da kuma kiyaye dokokin tsarin aikin jarida na kasashen nasu, ta yadda za su samu damar sanar da duniya abin da ke wakana a kasashensu ba tare da fuskantar wani tarnaki ba.